Hanyar Tuntubar Likita cikin sauki!

A wannan Manhaja ta KanoDoc Muna aiki da kwararrun likitocin dake kula da lafiyarku a manyan asibitocin da kuke zuwa. Kuma suna nan a shirye domin cigaba da duba lafiyar taku ta wannan manhajar.

Samun damar tuntubar Likita daga koina kuke cikin sauki ba tare da zuwa asibiti ba kafa-da-kafa.

Shin ko kun san

Amfanonin Manhajar KanoDoc?

Tuntubar Likita

Tattaunawa da kwararren likita cikin sauki daga ko ina.

Tattaunawa ta Video

Samun damar ganin likitan Ido da Ido ta hanyar Video.

Saukin ta'ammali

Amfani cikin sauki da wayar hannu da kuma kowanne lokaci.

Game da Manhajar KanoDoc

An bude shi ne sakamakon wannan yanayi da muka tsinci kanmu aciki na wannan annoba ta COVID19 (Coronavirus). Yawancin mutane basa son zuwa asibiti saboda tsoron kamuwa da cutar COVID19. Haka ma likitoci suna tsoron kamuwa da cutar daga wurin marasa lafiya.

Saboda wannan dalili ne aka bude wannan shafin domin a samu sauƙin haduwa tsakanin marasa lafiya da likita. Wannan zai taimaka wajen rage yaɗuwar wannan cuta.

Duk wanda yake bukatar ganin likita, ba lallai sai ya zo asibiti ba. Sai dai a halin neman taimakon gaggawa ko kuma haɗari. Kuma duk wanda za’a gani a wannan kafar sadarwa kyauta ne. 

Biyo mu a shafukan sada zumunta:

Idan kana jin wani alamun rashin lafiya

Tuntubi Likita yanzu!

Bada Tallafi

Za'a iya bada tallafin Kudi domin Taimakawa wajen tafiyar da wannan Manhaja.